1 Corinthians 14

Baye-bayen Annabci da kuma na Harsuna

1Ku bi halin ƙauna kuna kuma marmarin neman baye-bayen ruhaniya, musamman baiwar annabci. 2Gama duk wanda yake magana da wani harshe
Ko kuwa wani yare; haka ma a ayoyi 4, 13, 14, 19, 26 da 27
ba da mutane yake magana ba, sai dai da Allah. Hakika, ba wanda yake fahimtarsa; yana faɗin asirai ta wurin ruhu ne.
3Amma duk wanda yake annabci, yana magana ne da mutane domin yǎ gina su, yǎ ƙarfafa su, yǎ kuma yi musu taʼaziyya. 4Wanda yake magana da wani harshe kuwa, kansa yake gina, amma mai annabci, ikkilisiya ce yake gina. 5Zan so kowannenku yǎ yi magana da harsuna, sai dai zan fi so ku yi annabci. Wanda yake annabci ya fi wanda yake magana da harsuna, sai dai in ya fassara don ikkilisiya ta ginu.

6To, ʼyanʼuwa, a ce na zo wurinku ina kuma yin magana da waɗansu harsuna, amfanin me zan yi muku in ban zo muku da wani bayyani ko sani ko annabci, ko kuma kalmar koyarwa ba? 7Abubuwan nan marasa rai ma da sukan yi ƙara, kamar su algaita ko molo, in muryarsu ba ta fita sosai ba, yaya wani zai san abin da ake busawa ko kaɗawa? 8Haka ma in ba a busa ƙaho sosai ba, wa zai yi shirin yaƙi? 9Haka yake saʼad da kuka yi magana da waɗansu harsunan da ba a fahimta. In babu wanda zai san abin da kuke faɗi, za ka dai yi wa iska magana ne kawai. 10Ba shakka akwai harsuna iri-iri a duniya, duk da haka kowane a cikinsu yana da maʼana. 11To, in ban gane maʼanar abin da wani yake faɗi ba, ni baƙo ne ga mai maganar, shi kuma baƙo ne a gare ni. 12Haka yake a gare ku. Da yake kuna marmarin samun baye-bayen ruhaniya, sai ku ba da ƙarfinku ga yin amfani da waɗanda za su gina ikkilisiya.

13Saboda haka, duk wanda yake magana da harshe, sai yǎ yi adduʼa a yi masa baiwar fassara. 14Gama in na yi adduʼa da wani harshe, ruhuna ne yake adduʼa, sai dai hankalina bai amfana ba da yake ban gane ba. 15To, me zan yi? Akwai lokatan da zan yi adduʼa da ruhuna; akwai kuma lokatan da zan yi adduʼa da hankalina. Wani lokaci ya kamata in yi waƙa da ruhuna, a wani lokacin kuma in yi waƙa da hankalina. 16A cewa waɗansu baƙi suna cikin sujadarku, saʼad da kuke yabon Allah da ruhunku, yaya waɗanda suke tare ku za su fahimta, har su ce, “Amin,” da yake ba su san abin da kuke faɗi ba? 17Ko da yake kuna ba da godiya da kyau, amma wancan mutumin da yake tare da ku bai ginu ba.

18Na gode wa Allah, domin ina magana da harsuna fiye da ku duka. 19Amma a cikin ikkilisiya zan gwammace in yi magana da kalmomi biyar da za a fahimta don in koyar da waɗansu da a ce in yi magana da kalmomi guda dubu goma a wani harshe.

20ʼYanʼuwa, ku daina tunani kamar yara. Wajen mugunta ku zama jarirai, sai dai wajen tunaninku, ku zama manya. 21A cikin Doka yana a rubuce cewa:

“Ta wurin mutane masu baƙin harsuna
da kuma ta leɓunan baƙi
zan yi magana da waɗannan mutane,
amma duk da haka, ba za su saurare ni ba,”
Ish 28.11, 12

in ji Ubangiji.
22Harsuna fa alama ce ba ga masu bi ba, sai dai ga marasa bi. Annabci kuwa ga masu bi ne ba ga marasa bi ba. 23Saboda haka, in dukan ikkilisiya ta taru, kowa kuma yana magana da waɗansu harsuna, sai waɗansu jahilai ko waɗansu marasa bi suka shigo, ashe, ba za su ce kuna hauka ba? 24Amma in wani marar bi ko jahili ya shigo saʼad da kowa yana annabci, sai maganar kowa ta ratsa shi, za su shawo kansa yǎ gane cewa shi mai zunubi ne saboda abin da kowa yake faɗi, 25asirin zuciyarsa kuma su bayyana a fili. Don haka, zai fāɗi a ƙasa yǎ yi wa Allah sujada yana cewa, “Lalle, Allah yana cikinku!”

Tsarin Sujada

26Me za mu ce ke nan ʼyanʼuwa? Saʼad da kuka taru, wani yakan yi waƙa, wani koyarwa, wani wahayi, wani yin magana da wani harshe, wani kuma fassara. Dole ne a yi duka don gina ikkilisiya. 27In kuwa waɗansu za su yi magana a wani harshe, to, kada su fi mutum biyu ko uku, kuma a yi bi da bi, wani kuma yǎ fassara. 28In babu mai fassara, sai mai magana yǎ yi shiru a cikin ikkilisiya, yǎ yi wa kansa magana da kuma Allah.

29Annabawa biyu ko uku za su iya yin magana, sauran kuma sai su auna a hankali abin da aka faɗa. 30In kuma wahayi ya zo wa wani da yake zaune, sai mai magana na farko yǎ yi shiru. 31Dukanku kuna iya yin annabci bi da bi, domin kowa yǎ sami koyarwa da ƙarfafawa. 32Annabawa suna da iko a kan ruhohinsu. 33Gama Allah, ba Allah mai sa rikicewa ba ne, sai dai mai salama.

Kamar yadda yake a dukan ikkilisiyoyi na tsarkaka,
34ya kamata mata su zauna shiru a cikin ikkilisiyoyi. Ba su da izinin yin magana, sai dai su yi biyayya yadda Doka ta faɗi. 35In suna so su yi tambaya game da wani abu, ya kamata su tambayi mazansu a gida, domin abin kunya ne mace ta yi magana a cikin ikkilisiya.

36Shin, a kanku ne maganar Allah ta fara? Ko kuma a gare ku ne kaɗai ta iso? 37In wani yana tsammani shi annabi ne, ko yana da baiwar ruhaniya, bari yǎ gane cewa abin da nake rubuta muku umarnin Ubangiji ne. 38In ya ƙi kula da wannan, shi ma sai a ƙi kula da shi.

39Saboda haka ʼyanʼuwana, ku yi marmarin yin annabci, kada kuma ku hana magana da harsuna. 40Sai dai a yi kome daidai da kuma cikin tsari.

Copyright information for HauSRK